Jam’iyyar NNPP mai mulki a Kano ta kayyade kudaden tsayawa takarar shugaban karamar hukuma a kan Naira 500,000 da kuma naira 100,000 a matsayin kudin na gani ina so, yayin da masu neman tsayawa takarar kansiloli za su biya Naira 150,000 da kudin na gani ina so kan Naira 50,000.
Shugaban jam’iyyar a Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata.
- Zulum Ya Raba Wa Magidanta 10,000 Kayan Abinci A Mafa
- Adadin Masu Shigowa Da Fita Daga Sin Ya Karu A Watanni 7 Na Farkon Bana
Ya kuma bayyana aniyar jam’iyyar na tsayar da adalci ga duk masu son tsayawa takara a zaben kananan hukumomi da ke tafe a jihar.
Ya kuma yi kira ga masu sha’awar tsayawa takara da ke rike da madafun iko na zabe ko nadawa da su yi murabus daga mukaman kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC ta tanada.
Shugaban NNPP ya kara da cewa, Naira Miliyan 10 da KANSIEC ta kayyade ga masu neman takarar kujerar Shugaban karamar hukuma da kuma Naira miliyan 5 ga masu neman kujerar Kansiloli, wani abun a yaba wa hukumar ne.
A cewarsa, hakan zai sa mutane masu nagarta da hankali ne kadai za su fafata a zaben.