A wani mataki na magance tsadar kayan abinci a jihar, gwamnatin jihar Sokoto za ta sayar da tireloli 300 na shinkafa a farashi mai rahusa ga mazauna jihar.
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Ibrahim Dadi Adare, a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartaswar jihar ya ce, taron ya amince da sayen tireloli 300 na shinkafar da za a sayar wa mazauna jihar kan rangwamen kudi kusan kashi 55 cikin 100 idan aka kwatanta da farashin kasuwa.
- NNPP Ta Tsayar Da Naira 600,000 Kuɗin Takarar Shugaban Ƙaramar Hukuma A Kano
- Gundogan Ya Yi Ritaya Daga Buga Wa Jamus Kwallo
“Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Dr. Ahmed Aliyu, a wani shiri na rage radadin tsadar rayuwa, ta yanke shawarar siyo tireloli 300 na shinkafa domin siyarwa mazauna jihar kan farashi mai rangwame.
“Za a sayar da shinkafar ne ga kowace Unguwa 244 da ke fadin jihar”. In ji Adare
Ya ce, gwamnati ta ware fiye da Naira biliyan 14 don siyan shinkafar, tare da bayar da tabbacin cewa, za a kafa kwamitin da zai sanya ido kan aikin da kuma tabbatar da an cimma manufar shirin.