Gwamnatin tarayya ta amince da karin farashin kudaden fasfo din Nijeriya daga ranar 1 ga Satumba, 2024.
Kakakin Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), DCI Kenneth Udo, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya kara da cewa, matakin wani bangare ne na kokarin tabbatar da ingancin fasfo din Nijeriya.
- Ɗan Sarkin Gobir Da Aka Kashe Ya Kuɓuta Daga Hannun ‘Yan Bindiga
- An Kashe ‘Yan Bindiga Da Dama A Wani Artabu Da Sojoji A Filato
“Bisa sabon tsarin, Fasfo mai shafi 32 mai inganci na shekaru 5 wanda a baya ake biyan Naira 35,000 yanzu zai zama Naira 50,000; yayin da Fasfo mai shafi 64 mai ingancin shekaru 10, ya koma Naira 100,000 daga Naira 70,000.
“Amma farashin fasfo din bai sauya ba daga yadda yake a kasashen ketare,” in ji shi.
Ya kafa uzuri da nadama game da duk wani rashin jin daɗi da hakan ka iya haifarwa; Hukumar NIS na tabbatar wa ‘yan Nijeriya jajircewarta wajen tabbatar da gaskiya da samar da nagartaccen aiki a kowane irin lokaci.