Mazauna yankin unguwar Nepa, da ke garin Jos, Jihar Filato, sun cafke wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne bayan ya karɓi Naira miliyan 1.5 a matsayin kuɗin fansa inda suka miƙa shi hannun ’yan banga.
Kamar yadda wani ɗan banga a yankin wanda ya nemi a sakaye sunansa ya shaida, sun miƙa wanda ake zargin ga ofishin ’yansanda na Laranto da ke yankin Katako.
- Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Bincike Kan Rushewar Ginin Makarantar Saint Academy A Jos
- Duk Da Dokar Hana Fita, Matasa Sun Yi Fito Na Fito Da Jami’an Tsaro A Jos
Wanda ake zargin dai ya yi garkuwa ne da wasu ƙananan yara biyu kuma ya buƙaci Naira miliyan 1.5 daga iyayensu don fansa kana bayan ya karɓi kuɗin ya ci gaba da rike su.
Asirinsa ya tonu ne yayin da yaje wani kogo da ya ɓoye yaran inda mutanen da ke wucewa suka ji kukan yaran, suka ceto su, shi kuwa wanda ake zargin ya ranta a na kare tare da haure taga amma aka bi bayansa har aka yi nasarar kama shi.
Kakakin Ƴansanda na Jihar Filato, DSP Alabor Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce kawo yanzu wanda ake zargin ya na tsare a hannun rundundar kuma an same shi da tsabar kudi ₦1,492,000 kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kansa.