Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gudanar da wani taron manema labaru a yau Juma’a, don gabatar da karin bayani game da taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC dake tafe, inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Chen Xiaodong ya ce, bisa kudurin da bangarorin Sin da Afirka suka yanke tare, za a zartas da wata sanarwa ta musamman, da wani shiri kan ayyukan da za a gudanar, duk wajen taron kolin na FOCAC da zai gudana a birnin Beijing na Sin a farkon wata mai zuwa.
A cewar jami’in na Sin, ta wannan mataki ana fatan tabbatar da matsaya daya da bangarorin Sin da Afirka suka cimma, a fannonin neman zamanantarwa, da gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tsakanin bangarorin Sin da Afirka, da dai sauransu, gami da tsara ayyukansu na hadin kai masu inganci, wadanda za a gudanar da su cikin shekaru 3 masu zuwa.
Babban jami’in na Sin ya kara da cewa, dandalin tattaunawa na FOCAC, ya riga ya zama muhimmin biki dake alamtar hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, gami da zama abun koyi ga sauran sassan kasa da kasa, kan kulla huldar hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, da zurfafa hadin kan kasashe masu tasowa. (Bello Wang)