Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da Naira biliyan 3 domin tallafa wa jihar Kebbi da sauran jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa ciki har da babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda ministan kudi, Wale Edun ya sanar a Birnin Kebbi yayin wata ziyarar aiki da ya kawo ta kwana daya a jihar.
Edun, wanda ya duba gonakin shinkafa da ambaliyar ruwa ta shafa a Argungu, ya bayyana cewa, majalisar zartawa ta fadar shugaban kasa (NEC) ta amince da kuma mai da hankali wajen tallafa wa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa ciki har da babban birnin tarayya da naira biliyan uku domin dakile illolin ambaliyar ruwa da kuma bunkasa noman abinci.
- NYSC Ta Mayar Da Sansaninta Na Bauchi Zuwa Kwalejin Kangere
- Masarautar Gwandu Ta Farfaɗo Da Hawan Doki Na Shekara-Shekara
Majalisar zartawa ta tarayya ta amince da fitar da kudaden don tallafa wa manoman da suka yi asarar amfanin gona a sanadin ambaliyar ruwa, inji Edun.
Ya bayyana jin dadinsa da yadda kungiyar kamfanin Shinkafar Wacot ke gudanar da ayyukanta da kuma samar da aikin yi ga matasa a jihar Kebbi, inda ya ce, ta samar da dubunnan ayyukan yi da kuma yadda za ta ciyar da daukacin al’ummar kasar nan da abincin da suka dace.
Mista Edun ya kara da cewa, shugaba Tinubu na son taimakawa wajen fadada masana’antar shinkafa a jihar Kebbi domin bunkasa noman abinci, rage hauhawar farashin abinci, da samar da ayyukan yi.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya tallafa wa manoman shinkafa da ambaliyar ruwa ta shafa, inda ya bayyana cewa jihar Kebbi za ta iya ciyar da al’umma da tallafin da ya dace.