Akalla gidaje 14,940 ne ambaliyar ruwa ta lalata a jihar Sokoto.
Shugaban kwamitin kula da ambaliyar ruwa na jihar, Muhammad Bello Idris ne ya bayyana hakan yayin mika rahoton kwamitin ga gwamna Ahmed Aliyu a ranar Litinin.
- Inganta Raya Shawarar BRI Zai Zama Daya Daga Manyan Batutuwan Da Za A Tattauna A Gun Taron Kolin FOCAC Na Bana
- An Tura Tsohon Hadimin Tambuwal Zuwa Gidan Yari Kan Sukar Gwamnan Sakkwato Da Matarsa
A cewarsa, kauyuka 1,341 a fadin kananan hukumomi 22 ne suka fuskanci iftila’in ambaliyar ruwa a jihar a wannan shekarar.
Ya kara da cewa, gonaki 11,390 da amfanin gona masu yawa sun lalace a sakamakon ambaliyar.
Ya kuma kara da cewa, kimanin tafkuna 50 ne suka lalace, yayin da ruwa gurbatacce a wurare 250 ya tsaya cak ya daina gudanada, sannan kuma, magudanar ruwa mai nisan kilomita 60 ta lalace, duk sanadiyyar ambaliyar ruwan.
Kwamitin, ya ba da shawarar a ba da agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa tare da samar da kananan jiragen ruwa da rigunan ruwa ga al’ummomin da ke kewaye da koguna a jihar.
Har ila yau, kwamitin ya ba da shawarar cewa, ya kamata gwamnatin jihar, da masu ba da taimako na kasa da kasa, da su fara gina magudanar ruwa masu yawa, da kuma gyara wuraren da ake fama da matsalar zaizayar kasa da madatsun ruwa.
Gwamna Aliyu ya godewa kwamatin bisa aikin da suka yi tare da ba su tabbacin cewa, za a yi nazari da kuma yin aiki da shawarwarin da suka bayar.