Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya yi alkawarin sake gina gadoji da hanyoyin da ambaliyar ruwa ta lalata a kananan hukumomin Suru da Maiyama da sauransu.
Gwamnan Ya yi wannan alkawarin ne yayin wata ziyarar rangadin da ya kai yankunan da abin ya shafa a yau Laraba 28 ga watan Agusta, 2024.
Gwamna Nasir ya ziyarci gadar da ta wanke kan hanyar Suru-Kawara zuwa Dakingari inda ya duba gonakin shinkafa da suka lalace a karamar hukumar Suru. Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin sa na tallafa wa daukacin al’ummar jihar.
Gwamna dai ya tabbatar da cewa, gwamnatin jihar za ta gyara gadojin tare da sake gina hanyoyin, yayin da kuma za ta ci gaba da taimaka wa manoma wajen samar da abinci mai inganci da wadatar abinci a jihar.
Shugabannin kananan hukumomi da kuma dan majalisar dokokin jihar Mai wakiltar Suru, Hon. Faruku Maisudan, da dan takarar kujerar shugabancin Karamar Hukumar Suru a jam’iyyar APC, Mohd Lawal, sun yabawa Gwamnan bisa kokarinsa na ganin ya tallafa wa manoma da kuma mutanen da Ambaliyar ruwa ta shafa a duk fadin kananan hukumomi 21 na jihar.
Gwamnan ya kuma duba ababen more rayuwa da suka lalace a karamar hukumar Maiyama da suka hada da gada da ta wanke a kauyen Mayalo da ta hada kauyuka fiye da 20 da kuma wata gadar da ke kan hanyar Diggi. Ya kuma tabbatar wa al’ummar da abin ya shafa cewa, gwamnatin jihar za ta gyara ababen more rayuwa da suka lalace.
Gwamnan ya samu rakiyar mataimakinsa, Sanata Umar Abubakar-Tafida; sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Yakubu Bala-Tafida, da sauran jami’an gwamnatin jihar.