• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Shirye Sin Take Ta Tsara Yarjeniyoyin Ciniki Cikin ’Yanci Da Karin Kasashe Masu Tasowa

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 year ago
Sin

Maaikatar harkokin wajen Sin ta ce har kullum, kasar kan nace ga adawa da kariyar cinikayya, tare da nacewa ga inganta ci gaban duniya ta hanyar cinikayya da rage gibin dake akwai tsakanin manya da kananan kasashe. Kuma a shirye take ta tsara yarjeniyoyin ciniki cikin ’yanci da karin kasashe masu tasowa.

Kakakin maaikatar Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Alhamis.

  • Wang Yi Ya Yi Kira Ga Kasashe Mambobin BRICS Da Su Yi Hadin Gwiwar Shawo Kan Kalubalen Tsaro
  • Babban Sakataren Cibiyar ACBF Ya Yi Maraba Da Aniyar Kasar Sin Ta Tallafawa Noma Da Shawo Kan Kalubalen Sauyin Yanayi

Rahoton yanayin cinikayya a duniya na shekarar 2024 da hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) ta fitar a baya bayan nan, ya jaddada muhimmancin cinikayya wajen rage talauci da samar da ci gaba na bai daya, tare da bayyana cewa, tsananta kariyar cinikayya ka iya mayar da hannun agogo baya, ta fuskar rage gibin dake tsakanin masu hannu da shuni da masu karamin karfi, da shekaru 30. A cewar darakta janar ta WTO Ngozi Okonjo-Iweala, karuwa da kyautatuwar harkokin cinikayya ka iya ba karin mutane da yankunan damar dunkulewa zuwa karfin tattalin arzikin duniya.

LABARAI MASU NASABA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

A cewar Mao Ning, kasar Sin ta kasance babbar mai bayar da gudunmuwa ga aiwatar da harkokin cinikayya cikin ’yanci. Ta ce yayin taron kolin dandalin tattauna hadin kan Sin da Afrika, shugaban Sin Xi Jinping, ya gabatar da shawarwarin hadin gwiwa 10, ciki har da hadin gwiwa domin inganta ci gaban cinikayya tare da sanar da fadada bude kofar kasuwar kasarsa da soke haraji kan wasu kayayyaki da suka cancanci biyan kaso 100 bisa 100 na haraji, wadanda suka fito daga kasashen Afrika mafiya rangwamen karfi, inda kasar Sin ta zama babbar kasa mai tasowa ta farko, kuma mai karfin tattalin arziki a duniya, da ta aiwatar da wannan shiri. (Faiza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
Next Post
Kamfanin ‘Promasidor Nigeria’ Ya Kaddamar Da Sabuwar Garabasar ‘Onga Taste The Millions Promo’

Kamfanin ‘Promasidor Nigeria’ Ya Kaddamar Da Sabuwar Garabasar 'Onga Taste The Millions Promo’

LABARAI MASU NASABA

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.