A kwanan nan ’yan majalissar wakilan kasar Amurka sun sake bullo da wani mataki na gallazawa kasar Sin, inda a farkon makon nan suka amince da wasu kudurori na dakile damar kamfanonin kasar Sin daga shiga wasu ayyukan masana’antu, irin su na fasahohin amfani da halittu ko biotechnology. To sai dai kuma, masharhanta da dama na ganin hakan wani yunkuri ne kawai na kautar da tunanin Amurkawa daga tarin matsalolin da kasar suke ciki.
A zahiri take cewa wadannan kudurori maimaci ne na makamantansu da a baya Amurka ta gabatar, ta fakewa da cewa wai “Sin na zama barazana ga duniya”, wanda hakan ko shakka babu tunani ne kawai na farfado da yakin cacar baka.
- Wang Yi Ya Yi Kira Ga Kasashe Mambobin BRICS Da Su Yi Hadin Gwiwar Shawo Kan Kalubalen Tsaro
- Shugaba Xi Ya Yi Kira Da A Samar Da Sabbin Nasarori Wajen Kare Muhallin Halittu A Rawayen Kogi
Sai dai fa ga duk mai nazarin abubuwan da-ka-je-su-zo, ya san cewa ’yan siyasar Amurka na amfani da wannan rudani ne kawai, domin su rufe gazawarsu wajen shawo kan dimbin matsalolin da gwamnatin kasar ta gaza magancewa.
A halin da ake ciki Amurka na fama da tarin matsalolin bashi a cikin gida, da hauhawar farashin kayayyaki, da karancin guraben ayyukan yi, amma maimakon magance su, sai ’yan siyasar kasar ke ta mayar da hankali kan shafawa kasar Sin kashin kaji, da kirkirar karairayi marasa hujja, wadanda kuma ba za su taba warwarewa Amurkawa matsalolin dake addabar su ba.
Tuni dai kamfanonin Sin da wadannan kudurorin doka suka shafa irin su Wu Xi, AppTec da BGI Genomics, suka bayyana adawar su da matakin, suna masu bayyana hajojin da suke samarwa da marasa hadari ga tsaro, don haka matakin Amurka a wannan karo ba komai ba ne illa baiwa kasuwa kariya.
Kamar dai yadda masana da dama ke bayar da shawarwari, cewa a matsayin Sin da Amurka na manyan kasashe dake kan gaba a fannin karfin tattalin arziki, bai dace wani bangare ya rika nunawa dayan wariya, da danniya ta fuskar tattalin arziki ba. Kamata ta yi Amurka ta rungumi tafiya tare da Sin a matsayin ta hadin gwiwa, da cimma moriyar juna, ta yadda za a gudu tare a tsira tare.