Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga kwamitin tsaron majalissar da ya kara azama, wajen jawo hankalin sassa masu ruwa da tsaki a rikicin kasar Sudan, ta yadda za su kai ga warware sabanin dake tsakanin su ta hanyar siyasa.
Dai Bing ya yi kiran ne a jiya Laraba, yana mai sake bukatar bangarorin da ba sa ga maciji da juna a Sudan, da su sanya kasar su, da moriyar al’ummar ta gaban komai. Kana su martaba dokokin jin kai na kasa da kasa, da samar da cikakkiyar kariya ga fararen hula, da ababen more rayuwa da kaucewa kara barnata su.
- Ya Wajaba Amurka Ta Kauracewa Rura Wutar Cacar Baka Da Kokarin Illata Moriyar Kamfanonin Kasar Sin
- Wang Yi Ya Yi Kira Ga Kasashe Mambobin BRICS Da Su Yi Hadin Gwiwar Shawo Kan Kalubalen Tsaro
Daga nan sai ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su martaba ikon Sudan na mulkin kai da kare yankunanta, su kuma yi kokarin samar da karin tallafi, da hada kai da gwamnatin Sudan.
A hannu guda kuma, sassan dake gabatar da kudurori a kwamitin tsaron su martaba batutuwan da gwamnatin kasar ke nuna damuwa a kan su, da burikan gwamnatin, tare da kokarin shiga tsakani don cimma daidaito, tsakanin sassan kasar ba tare da shigar da burin kashin kai na siyasa ba. (Saminu Alhassan)