Hukumar da ke kula da albarkatun ruwa ta ƙasa (NHSA), ta yi hasashen cewa jihohin Nijeriya 11, za su iya fuskantar ambaliya sakamakon sakin ruwa madatsar ruwa ta dam ɗin Lagdo da ke ƙasar Kamaru.
Wata sanarwa da daraktan hukumar, Umar Muhammed, ya sanya wa hannu, ta ce mahukunta a ƙasar Kamaru sun ankarar da su cewa za su fara sakin ruwan dam ɗin Lagdo, daga ranar Talata 17 ga watan Satumba, 2024.
- ‘Yan Nijeriya Na Cikin Matsi Saboda Hauhawar Farashin Kayayyaki – Abdulsalami
- Sojoji Sun Cafke Masu Safarar Makamai 5 A Filato
Sun ce Æ™arfin ruwan zai karu a kwanaki bakwai masu zuwa la’akari da yadda ya ke kwarara daga kogin Garoua.
Jihohin da ta ambato ambaliyar za ta shafa sun haÉ—a da Adamawa da Taraba da Benue da Nasarawa da Kogi da Edo da Delta da Anambra da Bayelsa da Kuros Riba da Ribas.
Hukumar ta buÆ™aci gwamnati ta faÉ—akar da al’umma don É—aukar matakan da suka dace, na rage hatsarin ambaliyar saboda karuwar gudanar ruwa a manyan kogunan.
‘Yan Nijeriya dai musamman mazauna yankin kogin Binuwai sun daÉ—e suna fuskantar ambaliya daga tafkin Lagdo mai fadin murabba’i 586, a duk lokacin da aka saki ruwan.