Ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama ta raba babbar hanyar Maiduguri zuwa Damboa gida biyu a kusa da kauyen Dalwa da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno.
Lamarin wanda ya afku a ranar Talata, ya sa hanyar ba a iya wucewa, lamarin da ya tilasta wa masu ababen hawa yin amfani da wasu hanyoyi.
Da yake jawabi a wurin, shugaban karamar hukumar Damboa Hon. Ali Mohammed Kauji ya jaddada mahimmancin hanyar, wacce ta zama muhimmiyar hanyar da ta hada Kudancin Borno da babban birnin jihar, Maiduguri.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta gyara babbar hanyar da ta lalace domin saukaka zirga-zirgar ababen hawa domin amfanin jihar baki daya, yana mai cewa karamar hukumar Damboa na daya daga cikin babban yanki da ke samar da kayan abinci zuwa babban birnin jihar.