Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin ta ki amincewa da maganar jami’in kasar Amurka, na cewar Amurka na daukar kasar Sin a matsayin kalubale mafi girma, kasar Amurka tana duba yanayin kasa da kasa bisa manufofinta, da tsai da ra’ayinta kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, da maida kasar Sin a matsayin kalubale mafi girma. Kasar Amurka ta bayyana hakan ne domin ra’ayinta na kama karya, da tsara manufofi masu alaka da kasar Sin da dangantakar dake tsakaninta da Sin bisa kuskure. Hakan bai dace da moriyar jama’ar kasashen biyu da ra’ayin kasa da kasa ba.(Zainab Zhang)