Hukumar tattara alkaluman bayanan hidimomi na kasar Sin, ta ce ya zuwa karshen watan Agusta, yawan kamfanoni masu sarrafa hajoji na kasa Sin sun kai miliyan 6.03, karuwar da ta kai ta kaso 5.53 bisa dari kan adadin da ake da shi a karshen shekarar bara.
Cikin wannan adadi, akwai kamfanoni 515,300 masu nasaba da sabbin masana’antu, adadin da ya kai kaso 8.55 bisa dari na jimillar kamfanonin.
(Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp