An kaddamar da bikin murnar cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar Sin, wato jamhuriyar jama’ar Sin a birnin Ottawa, hedkwatar kasar Canada, bisa taken “A rubuce a sama”: Labari na da kasar Sin, a daren ranar 25 ga wannan watan nan da muke ciki, kuma an kaddamar da wannan biki a New York hedkwatar Amurka a ran 28 ga watan nan.
Babban rukunin gidan rediyo da talibiji na kasar Sin wato CMG, da ofishin jakadancin Sin dake kasar Canada ne suka yi hadin kai wajen gabatar da bikin. Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabarar da jawabi ta kafar bidiyo. Kuma wakilai kimanin 500 daga bangaren siyasa, da kasuwanci, da ilmi da watsa labarai na kasar Canada sun halarci bikin.
- Me Ya Sa Sin Da Sauran Kasashen Duniya Ke Cin Moriya Tare a Cikin Shekaru 75 Da Suka Gabata Tun Kafuwar Sabuwar Kasar Sin?
- Tinubu Ya Rantsar Da Kekere-Ekun A Matsayin Alkalin Alkalai Ta Nijeriya
Jakadan Sin dake kasar Amurka Xie Feng, da wakilai kimanin dari daga bangarori daban-daban dake sada zumunta da bangaren Sin da malamai da dalibai da dama sun halarci taron da aka gudana a New York.
A cikin jawabinsa, Mr. Shen Haixiong ya ce, ana daukar karin cudanyar kasa da kasa, da gaggauta yin shawarwari a bangaren al’adu da sa kaimi ga mu’ammalar al’umomi daban-daban da muhimmanci, ta yadda za a fahimci ruhin al’adun Sin, da ma hadin gwiwar al’umommin kasashen daban-daban wajen kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya cikin hadin kai.
Kafofin yada labarai 1255 daga kasashe ko yankuna 70 sun ba da labarai masu nasaba da bikin da aka gudana a New York, ciki har da Amurka, da Birtaniya, da Jamus, da Italiya, da Sifaniya, da Japan, da Koriya ta kudu da kungiyar kawancen kasashen Larabawa ko AL, da Indiya da Singapore da sauransu. (Amina Xu)