Kwanan baya, na kai ziyara kauyen Yugonglou, wanda ake masa lakabi da “Kauyen farko na shuka abarba”. Wannan kauye yana gundumar Xuwen ta birnin Zhanjiang na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin. Yawan abarba da kauyen ke samarwa a shekara ya kai fiye da kilogiram miliyan 40, wadda ke samarwa mazauna kauyen kudin shiga har fiye da dalar miliyan 14.
Sai dai a baya, kafin gwamnatin wuri ta jagoranci aikin kawar da talauci, abarba da suka nuna ta kan rube a gonaki, a maimakon ta samar da kudin shiga ga manoman.
- Me Ya Sa Sin Da Sauran Kasashen Duniya Ke Cin Moriya Tare a Cikin Shekaru 75 Da Suka Gabata Tun Kafuwar Sabuwar Kasar Sin?
- Amurka Ce Za Ta Yi Fama Da Mummunan Tasirin Tallafin Da Take Bayarwa Ga Neman ‘Yancin Taiwan
Sha’anin noman abarba ba kawai ya taimaka wajen kawar da talauci a wurin ba, har ma ta dogaro da sha’anin, gwamnatin wurin ta bunkasa sana’ar sarrafa abarba zuwa mabambantan kayayyaki, da kuma raya sana’ar yawon bude ido mai nasaba da al’adun abarba.
Bisa kididdigar da aka fitar, a shekarar 2023, yawan masu bude ido da gundumar Xuwen ta karba ya kai fiye da miliyan 1.6, adadin da ya karu da kashi 55%, kana yawan kudin shiga da aka samu ya kai kimanin dala miliyan 255, wanda ya karu da kashi 88%. Wannan wuri da ya shahara sosai ya dogaro da abarba, kuma ya raya tattalin arzikinsa bisa aikin kirkire-kirkire a bangaren yawon bude ido, ya kuma kara samar da yawan kudin shiga ga manoman wurin.
Yawan kudin shiga da manoma ke samu wani muhimmin ma’auni ne ta fannin tantance ainihin ci gaban da ake samu ta fuskar aikin raya kauyuka. A nan kasar Sin, hukumomin wuraren daban-daban suna nacewa ga daukar mabambantan matakai don kara kudin shigar manoma, hakan ya sa kauyuka kamar Yugonglong suka fita daga kangin talauci, tare da samun bunkasuwa sosai. Manoma na samun kudin shiga, wanda hakan ya kyautata zaman rayuwarsu, kana suke more rayuwarsu, wanda hakan abun fari ciki ne. (Mai zane da rubutu: MINA)