Tsohon gwamnan Jihar Kano, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya caccaki jam’iyyar APC mai mulki a karkashin Shugaban kasa Bola Tinubu, inda ya bayyana cewa manufofinta sun kara ta’azzara talauci da yunwa da kuma karuwar rashin tsaro.
Kwankwaso, wanda ya bayyana haka a taron kwamitin zartarwa na kasa karo na 7 na jam’iyyar NNPP a Abuja ranar Litinin, ya kuma bayyana PDP a matsayin matacciyar jam’iyyar da ke fama da rikicin cikin gida d take fuskanta a halin yanzu.
- Kasashe Fiye Da Dari Sun Ki Yarda Da Siyasantar Da Batun Hakkin Dan Adam
- Sin Ta Bukaci Kwamitin Sulhun MDD Da Ya Ingiza Sassauta Rikicin Lebanon Da Isra’ila
Yayin da yake bayyana NNPP a matsayin jam’iyyar da ta fi kowace jam’iyya tabaka a Nijeriya, ya ce ita ce jam’iyya daya tilo da za ta iya samar da shugabanci na gaskiya da zai magance bukatun ‘yan Nijeriya da kuma kawo musu dauki.
“Jam’iyyarmu tana aiki tukuru wajen ganin yadda za mu ingnta shugabancin da kowa zai gamsu da shi domin ci gabanmu.
“Tabbas muna samun hassada a wajen jam’iyyarmu tare da kai mana farmaki daga ciki da ma wajen jam’iyyarmu.
“Na yi matukar farin ciki duk da irin kalubalen da muke fuskanta, a yau jam’iyyarmu, ita ce jam’iyya mafi habaka a kasar nan.
“Na tuna lokacin da na ziyarci Katsina domin bude ofishinmu na jihar, a can na bayyana cewa jam’iyyun nan guda biyu, wato APC da PDP, musamman jam’iyyar PDP ta mutu kuma akwai matsaloli masu tarin yawa a cikin jam’iyyar.
“Na tabbata a lokacin da nake wannan furuci, da yawa daga cikinsu sun ga abin da ke faruwa a yau, wanda ake kokarin yi wa jam’iyyar gunduwa-gunduwa, jam’iyyar na cikin babbar matsala, don haka idan ba su fahimci wancan lokacin ba, to yanzu ina ganin sun fahimta kuma za su amince da abun da muke fada cewa jam’iyyar ta mutu.
“Jam’iyyar APC kamar yadda take a yau, za ka ga cewa ita ke shugabanci a sama, amma kuma al’ummar kasar nan gaba daya sun samu koma-baya.
“A wannan matakin ko sun yarda cewa suna yin kokari amma dukkanmu, musamman masu kada kuri’a a kasar nan mun yi imanin cewa ba su tabuka abin kirki ba, musamman idan aka yi la’akari da batun tsaro, talauci a kasar nan da kuma matsalar yunwa da muke gani a Nijeriya.
“Don haka, mun gode wa Allah da cewa jam’iyyun biyu duk sun durkushe, jam’iyyarmu ta NNPP tana habaka. Mun gode wa Allah Madaukakin Sarki a kan haka,” in ji Kwankwaso.