A halin yanzu jama’a na neman gano wane ne ke da gaskiya a tsakanin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da kuma hukumar gudanarwa ta jami’ar Jihar Bauchi wato Sa’adu Zungur (SAZU), kan ikirarin ajiye aikin manyan malamai masu matakin PhD su 30 bisa dalilin rashin albashi mai tsoka.
Shugaban shiyyar Bauchi na kungiyar ASUU, Namo Timothy, a wani taron manema labarai a makon jiya, shi ne ya sanar da cewa malaman sun ajiye aikinsu saboda rashin albashi mai kyau a jami’ar ta SAZU.
- Kaso 40 Na ‘Yan Nijeriya Na Samun Wutar Lantarki Fiye Da Awa 20 A Kowace Rana — Minista
- Kirkirar Kimiyya Da Fasaha Ta Kasar Sin Na Sa Kaimi Ga Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya
Sai dai nan take jami’ar ta ce lallai wannan ikirarin babu gaskiya a ciki, domin kuma babu wani malamin da ya ajiye aikinsa bisa hujjar rashin kyan albashi, malamai 30 ba su ajiye aikinsu a jami’ar ba.
Timothy ya lura kan cewa jami’ar na gab da rushewa sakamakon rashin iya kula da harkokin jami’ar da ma mambobinta.
Ya bukaci gwamnatin Jihar Bauchi da ta tashi tsaye wajen shawo kan tulin matsalolin da suke jami’ar muddin in ba ana son ruguza harkokin ilimi a jami’ar ba. Ya ce tsawon shekaru ana nuna halin ko’in-kula da jin dadi da walwala na malamai a jami’ar.
Ya koka kan cewa mambobin ASUU a jami’ar SAZU ba su da tsarin fansho kuma babu wani tanadi na in mutum ya rasu zai samu wani abu, don haka suka nuna cewa dole a dauki matakin gyara.
Sannan baya ga korafi kan karancin albashi mai tsoka, kungiyar ta ce mambobinta na fama da matsalar rashin samun alawus-alawus da wasu hakkoki da dama da aka kasa musu.
Auwal ya ce jami’ar SAZU ba ta amshi wani wasika na ajiye aiki daga wajen wani malami da ya bayar da hujjar cewa albashin da ke samu ya masa kadan ba.
Ya warware zare da abawa, inda ya ce, “Malamai masu matakin PhD shida (6) ne kawai suka ajiye aiki a tsawon shekaru biyu da suka wuce, kuma dukkanninsu sun ajiye aiki ne bisa dalilai na kashin kai ba wai ya shafi maganar albashi mai tsoka ba.”