Hukumar Alhazai ta Nijeriya, NAHCON ta bayyana cewa, maniyyatan Nijeriya 95,000 da suka halarci aikin hajjin shekarar 2023 za a mayar musu da kudi Naira 67,500 kowanne saboda rashin samun cikakkiyar kulawa a lokacin aikin hajjin da ya gabata.
Mai magana da yawun hukumar, Fatima Usara, ce ta bayyana hakan biyo bayan wani taron da aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata wanda hukumar NAHCON ta shirya.
- Gwamnati Ba Za Ta Ci Gaba Da Biyan Tallafin Aikin Hajji Ba – NAHCON
- Muna Tattaunawa Don Ganin An Tsagaita Wuta A Yakin Gabas Ta Tsakiya – Kamala Harris
A yayin taron, wanda kwamishinan ayyuka na NAHCON, Prince Anofi Olanrewaju Elegushi ya jagoranta, an tattauna wasu sabbin tsare-tsare na ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudi Arabiya (MoHU) da kuma shawarwarin NAHCON na baya-bayan nan.
Elegushi ya kuma yi tsokaci kan gyare-gyaren aikin Hajji na shekarar 2025, inda ya bayyana cewa, za a rage yawan kamfanonin da za su gudanar da aikin Hajji daga 20 zuwa 10.