Shugaban ƙasa Bola Tinubu, na shirin zuwa birnin Paris na kasar Faransa daga Birtaniya, a kowane lokaci daga yanzu don wata muhimmiyar hulɗa da ba a bayyana ba.
Wani makusancin siyasa ga shugaba Tinubu, kuma tsohon abokin takararsa Ibrahim Kabir Masari, ne ya bayyana hakan a yammacin yau Juma’a.
- Kotu Ta Hana Hukumar EFCC Binciken Jihohi 10 — Olukoyede
- Tsakanin Kwankwaso Da Obi, Waye Babba A Siyasa?
Idan ba a manta ba Shugaba Tinubu ya tafi Landan ne a ranar 2 ga watan Oktoba, 2024, don hutun mako biyu, kamar yadda wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar wanda ya ce hakan na daga cikin hutunsa na shekara kuma shugaban zai dawo gida Nijeriya da zaran hutun ya ƙare.
Wannan dai shi ne karon farko da shugaba Tinubu, ya tafi hutu tun bayan hawan sa mulki a watan Mayun 2023, duk da cewa ya yi tafiye-tafiyen kasashen waje da dama daga lokacin zuwa yanzu.
Bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki na 1999, akwai buƙatar shugaban ƙasa ya rubuta wa majalisar dokokin ƙasa, tare da sanar da ita shirinsa na tafiya hutu wanda babu tabbas na cewa Shugaba Tinubu ya yi hakan ko bai yi ba.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Juma’a, Masari wanda ya ziyarci shugaba Tinubu a Landan, ya bayyana cewa za su yi tafiya tare da shugaban kasar zuwa Faransa.