Wata babbar kotu da ke a Garin Argungu a Jihar Kebbi, ta yanke wa wani matashi mai suna Badamasi Abdullahi Mai shekaru 25 hukuncin daurin rai da rai a gidan gyaran hali, bisa samun sa da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 16 fyade.
An samu matashin da laifin ne a karkashin sashe na 259(1) na dokar laifuka ta Jihar Kebbi, 2021.
Lauyoyin gwamnati masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu biyar tare da gabatar da takardun shaida guda bakwai don tabbatar da laifin da ake zarginsa da aikatawa a cikin shari’ar.
Kamar yadda bayanan a gaban kotun suka nuna, Badamasi Abdullahi, babban aboki ne ga yayan yarinyar da aka yiwa fyade, amma duk da kusancin sa da yayanta bai hana shi ya yi mata fyade ba.
Haka kuma ya aikata laifin ne bayan ya dawo daga siyan taba cigari.
Duk da rokon da ta yi masa cewa tana jinin haila, Badamasi ya kai mata hari tare da yi mata fyade.
Mai shari’a Shamsudeen Jafar ne, ya zartar da hukuncin, inda ya bayyana cewa shaidanni guda biyar da takardun shaida guda bakwai duk sun bayyana shaidar aikata laifin na fyade da ake zargin Badamasi Abdullahi da aikatawa a cikin watan fabrairu 2024 .
Haka kuma masu bayar da kariya sun kasa gabatar da kwakwaran hujjoji ko bayanai da za su soke sahihancin shaida da hujjojin da masu gabatar da kara suka gabatar a gabanta,” in ji kotu a yayin gabatar da hukuncinta”
Kotun ta ci gaba da bayyana cewa “A bisa sashe na 259 (1) na dokar laifuka ta jihar Kebbi, 2021, Badamasi Abdullahi, namiji, dan shekaru 25 da haihuwa a duniya kotu ta kama ka da laifin yi wa yarinya ‘yar shekara 16, bisa ga haka kotu ta yanke maka hukuncin daurin rai da rai zuwa gida gyaran hali.
A yayin da yake kare kansa, Badamasi Abdullahi ya kira shaida guda daya kuma ya ba da shaidar kansa.
Sai dai masu gabatar da kara sun tabbatar da duk wani abu da ke tattare da aikata laifin fyade, wanda ya kai ga daurin rai da rai ga wanda a ke tuhumar.