A ranar Lahadin makon jiya ne aka gabatar da taron Mauludi a karon faro a garin Orimerummu da ke karamar hukumar Owode ta Jihar Ogun.
Taron wanda ya samu halartar al’umma da dama daga ciki da wajen jihar an shirya ne a karkashin jagorancn manya-manya malamai daga bangaren Hausawa da Yarbawa wanda hakan ke nuna irin zaman lafiyar da fahimtar juna da ake da shi a tsakanin al’ummun biyu.
- Maulidi: Fityanul Islam Ta Jajanta Wa Al’ummar Borno Kan Ibtila’in Ambaliyar Ruwa
- Jirgin Ruwa Dauke Da ‘Yan Maulidi 200 Ya Nutse A Neja
A tsokacinsa, Malam Ibrahin Shua’aibu dan asalin karamar hukumar Musawa ta Jihar Katsina, ya nemi matasa su himmatu da neman ilimi su kuma yi biyaya ga iyaye don da shi ne za a samu albarka a rayuwa, ya kuma karfafa su a kan soyayya ga Manzon Tsira (SAW).
Haka kuma Alhaji Bala Abubaka dan asalin karamar hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato.ya yi godiya a kan yadda al’umma suka samu halartar taron musamman wadanda suka zo daga Legas, Shagamu, Mowe, da Owode ya kuma yi addu’ar yadda suka zo lafiya Allah ya mayar da kowa gidansu lafiya, ya yi addu’a Allah ya bar zumunci., ya kuma ce wannan mauludin shi ne karo na farko da al’ummar garin suka shirya. Ya kuma ba dukkan wadanda basu samu sakon gayyatarsu ba hakuri, ya ce, wannan ya faru ne sadoda an shirya taron ne a a kurarren lokaci.
Shi kuwa Abdullahi mai Kano ya nmuna jkin dadinsa a kan yadda aka samu halartar manyan baki kamar, Khalifa Malam Muhammadu daga Shagamu da kuma Sarkin Shagamu da mayan Malamai daga garin Ibako. Ya kuma nuna farin cikinsa a kan yadda aka yi taron aka gama lafiya, a kan haka ya nemi matasa su rike koyarwar manzon Allah a dukkan al’amurran da suka sa a gaba.
Ta bangaren Yarbawa an samu halartar Alhaji Said, da Shekh Abdulkadir Alnagari da sheikh Abu AbudulKari da Shekih Abdalla, kuma sun bayar da gudummawa mai muhummanci, sai kuma malami mai wa’azi da ya zo daga nesa Malam Mahmud, sai Malam Abdulkadir da kuma Zakira daban daban duk sun gudanar kasida, ‘Muna godiya gare su”