Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta bukaci mazauna garin Saminaka da su yi watsi da tashe-tashen hankula, su rungumi zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaben kananan hukumomin da ke tafe a ranar 19 ga Oktoba, 2024.
Dakta Hadiza Balarabe ta bayyana haka ne a karshen mako a lokacin da ta jagoranci tawagarta zuwa Saminaka domin gudanar da yakin neman zaben jam’iyyar APC a karamar hukumar Lere gabanin zaben kananan hukumomi da za a yi a jihar Kaduna.
- Dan Nijeriya Ya Samu Kyautar Dala 600 Bayan Lashe Gasar Mr. Olympia A Amurka
- Haɗama, Son Kai Da Jahilci Ne Sanadin Wahala A Nijeriya – Obasanjo
Ta yi kira ga mazauna yankin da su zabi Hon. Jafaru Ahmed, dan takarar kujerar shugaban karamar hukumar Lere a jam’iyyar APC mai mulki.
Hakazalika Dr. Balarabe tare da tawagarta ta karkata akalar jirgin yakin neman zaben zuwa karamar hukumar Soba daga Saminaka, Lere zuwa Tudun Saibu na Maigana a cikin garin Soba domin nuna goyon bayansu ga dan takarar APC a zaben kananan hukumomin da ke tafe.
“Ina gabatar da Honorabul Muhammed Shehu Lawal (MOLASH) wanda ya tsaya takarar shugaban karamar hukumar Soba,” inji ta.
A cewarta, “MOLASH mutum ne na jama’a.”
A nasa jawabin, dan takarar, Hon. MOLASH ya yabawa jama’a tare da gode musu kan soyayyar da suka nuna masa.