Hukumar Kula da Shige da Fice (NIS) reshen Jihar Bayelsa za ta fara bayar da sabon ingantaccen fasfo, a wani yunƙuri da hukumar ke yi na sauyawa daga tsohon yayi na fasfon zuwa sabon da aka samar.
Shi dai sabon fasfon yana ƙumshe da abubuwa na tsaro sama da 25, kana an tsara shi a bisa ingancin da duniya ta amince da shi wanda sannu a hankali zai maye gurbin tsohon samfurin fasfon da ake bayarwa.
Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a Bayelsa, ta shawarci masu neman fasfo a yankin jihar su bi ƙa’idar da hukumar ta sa wajen gabatar da buƙatarsu ta hanyar amfani da sadarwar intanet a dukkan matakan da ake bi tun daga cike takardar nema zuwa biyan kuɗi da ɗaukar hoto da sanin ranar karɓa wanda hakan zai hana mai nema faɗawa hannun bara-gurbi masu tatsar kuɗi.
Ita dai NIS ta duƙufa wajen ganin mutane suna samun fasfo ba tare da katsalandan daga wani ba. Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola tare da Kwanturola Janar na NIS Isah Jere Idris za su ƙaddamar da babbar cibiyar fasfon a Jihar Ribas wadda za ta karaɗe ofisoshin fasfo na Jihohin Akwa-Ibom, Bayelsa, da Kuros Ribas.
Sabon ingantaccen fasfon dai yana da tsare-tsare na musamman da aka kasafta zuwa matakai guda uku. Akwai mai shafi 32 da yake aiki na tsawon shekara 5, sai mai shafi 64 da yake aiki na tsawon shekara 5 da kuma mai shafi 64 da yake aiki na tsawon shekara 10.
Hanya mafi sauƙi da mutum zai bi ya nemi fasfon ita ce ya shiga adireshin intanet na: passport.immigration.gov.ng, yana shiga zai ga fom sai ya cike tare da biyan kuɗi, duka dai ta intanet. Daga nan sai ya sauke takardar shaidar biyan kuɗi da ta lokacin da aka ba shi na zuwa ɗaukar hoto tare da wallafawa.
Mutum zai ziyarci ofishin fasfo ne kawai a ranar da aka ce ya je, sai ya tafi da abubuwan da aka ce ya tanada ciki har da takardar shaidar biyan kuɗinsa.
Wajibi ne dai ga kowane mai neman fasfo ya yi amfani da lambarsa ta shaidar ɗan ƙasa wajen neman fasfo. Wa’adin samun fasfo ga sabbin shiga shi ne mako shida, yayin da na waɗanda za su sabunta kuma bai wuce mako uku ba.
Domin ƙarin bayani ana iya kiran wannan lambar: 08021819988 ko a ziyarci adireshin NIS na intanet ta: www.immigration.gov.ng
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp