Gwamnatin Jihar Taraba ta yi watsi da jita-jitar da ake yadawa na cewa za ta rushe fadar masarautar Sarkin Takum da babban masallacin Juma’a, inda ta ce labarin bashi da tushe balle makama.
Gwamna Agbu Kefas, ta bakin kwamishiniyar yada labarai ta jihar, Zainab Usman Jalingo, ta bayyana ikirarin a matsayin mara tushe, inda ta bayyana cewa ana shirin ne domin neman tada zaune tsaye.
- Magoya Baya Sun Kori Kwankwaso Daga NNPP, Sun Kona Jar Hula A Jihar Neja
- Ko Za A Kore Ni Daga APC Ba Zan Daina Fadar Gaskiya Ba – Ndume
“Wadannan zarge-zargen kwata-kwata ba gaskiya ba ne, mu mun mayar da hankali ne kan samar da shugabanci na gari da ci gaba mai dorewa ba batun addini ko kabilanci,” in ji Jalingo.
Ta kuma bukaci jama’a da su yi watsi da wannan jita-jitar, wadanda ta danganta su ga masu neman kawo hargitsi.
Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnati na samar da zaman lafiya, hadin kai, ci gaba, da adalci ga daukacin mazauna jihar.