Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci lardin Fujian da ke gabashin kasar Sin da ya taka rawar majagaba a kokarin zamanantar da kasar Sin, ta hanyar tsayawa tsayin daka kan manufofin samun ci gaba.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na sojan kasar, ya bayyana hakan ne yayin rangadin da ya kai lardin da ke gabar teku a ranakun Talata da Laraba. (Yahaya)