Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa kasar Sweden a ziyarar kwanaki 2 domin wakiltar Nijeriya a huldar kasashen biyu.
Mataimakin shugaban kasar, yayin da zai wakilci shugaba Tinubu a ziyarar aiki, zai tattauna da manyan jami’an gwamnati, ciki har da ganawa da Gimbiya Victoria ta Sweden (mai jiran gado) da kuma firaministan kasar Sweden.
- CAF Ta Ɗage Wasan Super Eagles Da Libya
- Gidauniyar Sam Nda-Isaiah Ta Miƙa Miliyan 250 Da Gwamna Bago Ya Ba Ɗan Adaidaita Sahun Kano
Shettima, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, ya fitar, zai yi amfani da ziyarar ne domin lalubo damammakin karfafa hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da Sweden a fannoni kamar bangaren sadarwar zamani (ICT), kirkire-kirkire, ilimi, na’urorin zamani, sufuri, hakar ma’adinai, da kuma noma.
Shettima zai kuma gana da manyan masu ruwa da tsaki a bangaren gwamnati da masu zaman kansu.