Mujjallar Forbes da ke binciken kwa-kwaf kan masu kudi a duniya ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasan kwallon kafa da sukafi karbar albashi a duniya.
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr, Cristiano Ronaldo da fitaccen dan wasan Inter Miami Lionel Messi ne ke jagorantar jerin yan wasan.
- Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnoni Na Tozarta Dimokuradiyya – Jam’iyyun Adawa
- Babban Layin Samar Da Wutar Lantarkin Nijeriya Ya Lalace Sau 7 A 2024
Dukkanin ‘yan wasan biyu ana daukar su a matsayin manyan ‘yan wasan kwallon kafa biyu da suka samu daukaka a tarihin wasan kwallon kafa.
Ronaldo ne na daya a jadawalin inda yake samun dala miliyan 285 a duk shekara, dan wasan mai shekaru 39 yana karbar dala miliyan 220 a duk shekara a matsayin albashi daga Al-Nassr, yayin da sauran ke zuwa daga tallace-tallace.
A matsayi na biyu kuwa Messi ne, inda dan kasar Argentina yake daukar dala miliyan 135 gaba daya, daga cikin kudin dala miliyan 60 daga albashi ne kuma sai dala miliyan 75 daga tallace-tallace.
Kamar yadda jadawalin ya nuna ‘yan wasan da ke buga gasar Saudi Arabiya ne, suka mamaye jerin sunayen, sauran sun hada da Neymar na Al-Hilal ($ 110m), Karim Benzema Al-Ittihad ($ 104m) da Sadio Mane na Al-Nassr ($ 52m).
‘Yan wasan Real Madrid biyu Kylian Mbappe ($90m) da Vinicius Junior ($55m) su ne kawai wakilai daga LaLiga,yan wasan Premier uku Erling Haaland ($ 60m), Mohamed Salah ($ 53m), da Kevin De Bruyne ($ 39m) sune cikon jerin sunayen ‘yan wasa 10 da suka fi samun albashi a duniya.