Kasar Sin ta fitar da wasu ka’idoji, irinsu na farko domin ganowa da maganin cutar kiba fiye da kima daga bangarorin kwarewa daban-daban.
Hukumar kula da lafiya ta kasar Sin wadda ta jagoranci tsara ka’idojin da aka fitar jiya Alhamis, ta ce ka’idojin sun kunshi bangarorin kwarewa daban daban, domin daidaita dabarun ganowa da maganin cutar ta kiba da kuma tabbatar da inganci da amincin kiwon lafiya.
- Xi Zai Halarci Taron Kolin BRICS Karo Na 16 A Rasha
- Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Ayyukan ‘Yan Ta’adda A Arewa Maso Yamma
Ka’idojin na da nufin magance rashin daidaito a bangarorin ganowa da nau’i da matakan cutar ta kiba fiye da kima. Bangaren maganin cutar ya hada da dabarun daidaita halayya da tunani da motsa jiki, da yanayin cin abinci mai gina jiki da magunguna da rage kiba da tiyata da kuma wasu dabaru daga likitanci gargajiya.
Kasar Sin ta shafe shekaru da dama tana gwagwarmayar ciyar da al’ummarta. Kuma rashin sinadaran gina jiki, ita ce babbar damuwar da iyalai da dama ke da ita kafin kaddamar da manufar bude kofa da gyare-gyare a gida a karshen shekarun 1970. Kiba fiye da kima, ya zama wani sakamako na ingantuwar yanayin rayuwar jama’a a kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)