Kasar Sin na da burin samar da maaikatan masanaantu a mataki mafi girma da nufin ba da taimakon hazaka da fasaha mai karfi don gina babbar kasa, da kuma sake farfado da al’ummar Sinawa ta hanyar zamanantar da kasar Sin.
Ta hanyar zurfafa gyare-gyare a fannin gina maaikatan masanaantu, kasar na da niyyar samar da kwararrun yan kwadago kimanin 2,000 a matakin kasa, 10,000 a matakin larduna, da 50,000 a matakin birane, wadanda ke da ilimi sosai kuma masu basira da fasahohin kirkire-kikire nan da shekarar 2035, bisa ga kaidojin da kwamitin kolin jamiyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar suka fitar.
Don dacewa da bukatun sabbin masanaantu, kasar za ta habaka ilimin sanaoin zamani, da kara kokarin habaka hazaka tare da cikakkiyar kwarewar fasaha, da kuma daidaita tsarin horar da sanaoi na tsawon rayuwa ga maaikatan masanaantu, da nufin samar da gwanintar da ake bukata cikin gaggawa don bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da sa kaimi ga samar da ci gaba mai inganci, bisa ga kaidojin. (Yahaya)