Wasu sabbin alkaluma sun nuna cewa, kasar Sin ta samu karin kyautatuwar iska, da ruwa, a watanni 9 na farkon shekarar nan ta 2024.
Kakakin ma’aikatar lura da muhalli, da muhallin halittu na kasar Sin Pei Xiaofei ne ya shaidawa ‘yan jarida labarai hakan, yayin taron manema labarai na Talatar nan, inda ya ce tsakanin watan Janairu zuwa Satumban bana, matsakaicin adadin ma’aunin ingancin iska na PM2.5 a biranen kasar Sin 339, masu matsayi sama da gunduma, ya kai micrograms 27 kan duk kyubik mita, adadin da ya ragu da kaso 3.6 bisa dari kan na makamancin lokaci na bara.
- Yaya BRICS Za Ta Kara Taka Rawa Wajen Ingiza Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa
- Xi Ya Tafi Halartar Taron Kolin BRICS Karo Na 16 A Rasha
Kaza lika, Pei ya ce adadin ranaku masu kyawun yanayin iska a wadannan birane, cikin wannan adadin watanni ya kai kaso 85.8 bisa dari, karuwar da ta kai kaso 1.6 bisa dari kan na makamancin lokaci na bara.
Bugu da kari, jami’in ya ce kaso 88.5 bisa dari na yankunan da aka nazarta, na da ingancin ruwa madaidaici, wanda ya haura mataki na 3, cikin matakai 5 da kasar ta tsara don auna ingancin ruwa, adadin da shi ma ya karu da kaso 1.4 bisa dari kan na makamancin lokaci na bara. (Mai fassara: Saminu Alhassan)