Hukumar bunkasa zuba jari ta jihar Kebbi (KIPA) ta nemi hadin gwiwa da masana’antar sufurin jiragen sama ta kasa, FAAN a ranar Talata domin jawo hankalin masu zuba jari zuwa Jihar.
Darakta Janar na KIPA, Dakta Mohammed Kabir-Kamba, ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Manaja kuma Sakatare dindindin na FAAN a filin jirgin sama na kasa da kasa na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi.
- An Fitar Da Tsarin Manhajar Wayar Salula Na Farko Na Sin A Hukumance
- Hadin Gwiwar BRICS Ya Samu Ci Gaba Mai Dorewa Bisa Jagorantar Shugaba Xi Jinping
Kamba ya jaddada muhimmancin samar da yanayi mai kyau na zuba jari a jihar Kebbi. “Mun shirya gina reshen hukumar bunkasa zuba jari ta jihar Kebbi. Kuma wani bangare na abin da muke yi shi ne, samar da hadin gwiwa, hada kai da kulla alaka da kungiyoyi masu zuba jari kamar masana’antar jiragen sama, da kuma tashar dakon kaya na tudu wato cargo” in ji shi.
Babban daraktan ya bayyana cewa, filin jirgin yana da matukar muhimmanci, domin galibin mutanen da ke wucewa manyan mutane ne masu karfin saka hannun jari a jihar Kebbi. Ya bayyana fatansa cewa, hadin gwiwa da hadin kai za su cike gibin da ke tsakanin hukumomin biyu tare da inganta jihar.
Dokta Kabir-Kamba ya yi karin haske kan muhimman wuraren da jihar Kebbi ta ke a kasuwar Afirka ta Yamma, inda ake samun sama da mutane miliyan 600 a kasuwar. Ya kuma jaddada cewa, hukumar ta mayar da hankali wajen jawo hankalin masu zuba jari a fannin noma, makamashi, sauyin Yanayi, kiwon lafiya da ilimi.
Da yake mayar da martani, Manajan Filin Jirgin saman kuma Sakatare na dindindin a jihar, Alhaji Habib Muhammad-Sabi ya yaba da ziyarar da Dakta Kamba ya kai masa, ya kuma ba shi tabbacin yin hadin gwiwa mai inganci.