Twagar Super Eagles ta Nijeriya ta tashi daga matsayi na 39 zuwa na 36 a jerin sunayen tawagar maza da suka iya taka leda a duniya na hukumar FIFA.
An fitar da sabon jadawalin na duniya a yau Alhamis, 24 ga watan Oktoba kamar yadda aka buga a shafin intanet na hukumar ta FIFA.
- FIFA Ta Dakatar Da Martinez Daga Buga Wasanni Biyu
- Kungiyoyi Sun Maka FIFA A Kotu Saboda Yawan Wasanni
A nahiyar Afrika kuma, Super Eagles ta tashi daga matsayi na shida zuwa na huɗu, inda ta ke a bayan Morocco, wacce ita ce ta daya a Afirka kuma matsayi na 13 a duniya, Senegal da kuma ƙasar Masar (30).
Jamhuriyar Benin da za ta karɓi baƙuncin Eagles a wasa na 5 a rukunin D na wasannin neman gurbin shiga gasar AFCON 2025, ta koma matsayi na 95, Rwanda kuma ta koma matsayi na 126, yayin da Libya ta koma ta 122.
A halin da ake ciki, zakarun gasar cin kofin duniya, Argentina har yanzu su ne kan gaba a matsayi na ɗaya yayinda ƙasashen Faransa da Spain ke matsayi na biyu da na uku bi da bi, za a buga jadawalin duniya na FIFA na gaba a ranar 28 ga Nuwamba, 2024.