Kamfani LEADERSHIP da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Nasarawa sun kaddamar da ba da horo ga matasa a fannin koyar da sana’o’i daba-daban a karkashin shirin Gwamnatin Shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu na tsamo ‘yan Nijeriya miliyan biyu daga kangen talauci.
Matasa 100 ne suka ci gajiyar shirin wadanda dukkaninsu mata ne da suka fito daga Jihar Nasarawa. An gudanar da wannan horo ne a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda aka koyar sana’o’in da suka hada da; yadda ake noman kifin da kaji da yadda ake ciyar da su, kiwon zuma, koyar da ilimin fasahar sadarwa. Sauran sana’o’in sun hada koyar da sana’ar takalma, yadda ake yin kamfala, koyar da sana’ar takalma.
- Sarki Sanusi II Zai Naɗa Babban Ɗansa A Matsayin Ciroman Kano
- Abin Da Ya Sa Ƙasashen Duniya Suka Gina Majalisar Ɗinkin Duniya – Sakatare Janar
Da yake magana a yayin kaddamar da shirin, Babban Editan Rukunin Kamfanin LEADERSHIP Mr Azu, ya bayyana jin dadinsa tare da gamsuwarsa da wannan shiri, inda ya ce “Ko shakka babu yau LEADERSHIP muna cikin farin ciki domin kaiwa ga wannan matakin farkon cikin abin da muke buri.”
“Bugu da kari, muna matukar godiya ga Zababben Gwamnan Jihar Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi A Sule, sakamakon amincewa da ya yi da wannan muhimmin shiri da zai taimaka wajen tsamo ‘yan Nijeriya miliyan biyu daga kangin talauci, tare da zabo mutum 100 wadanda za su amfana da shirin bisa dacewa kuma cikin gaggawa, babu shakka wannan ya tabbatar da nuna sadaukar da kai cikin ayyukan da suka shafi al’umma,”in ji shi.
Ya ba da misali kan wasu adadi da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBA ta fitar inda ta bayyana cewa, ‘yan Nijeriya yawan ‘yan Nijeriya marasa aikin yi ya kai kashi 5.3 cikin 100, kuma wannan kididdiga ba ta tsaya a miliyoyin ‘yan Nijeriya da ba su da aiki yi kadai ba, lamarin ya shafi iyalai da ke fadin kasar nan wadanda ba sa iya sayawa ‘ya’yansu barin biredi, ko mudun shinkafa ko madara.
A karshe ya bayyana fatansa akan wannan shiri, inda ya ce wannan horarwa za ta iya hada abubuwan da aka koya muku domin amfanin kanku.
Wakilinmu ya samu zantawa da wasu daga wadanda suka ci gajiyar shirin inda suka bayyana masa irin godiya da farin ciki gami da addu’ar da suka yi Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da bullo da shirin. Sannan kuma suka nuna godiya ga Gwamnatin Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya A A Sule bisa jajircewarsa wajen ganin ya zama na farko wajen aiwatar da wanna shiri a fadin kasar nan.
Fatima Musa daga cikin wadanda suka gajiyar wannan shiri wadda ta zo a bangaren wadanda aka koyawa sana’ar Rini da Bugu, wato yadda za su sarrafa farin kaya ya koma launin Kamfala. Ta yi godiya ga Gwamantin A A Sule bisa wannan dama da ta bata, inda ta ce ba ta tsammanin za ta tsinci kanta a wannan shiri ba. “ A yanzu na samu sana’ar da zan dogara da kaina kuma ina fatan nan da wani lokaci in koyawa wasu suma su tsaya da kafarsu.
Haka ita ma Aisha Yakubu, na daga cikin wadanda suka gajiyar wannan shirin na koyon sana’o’i, wacce ta samu horo kan yadda za a sarrafa abincin kaji da kifi, da kuma yadda ake nomansu, cewa ta yi, babu abin da za su cewa gwamnatin mai girma A A Sule sai dai addu’ar Allah ya sa ya gama da duniya lafiya.
Ita kuwa Hajiya Amina Muhammad wadda ta samu shiga cikin shirin wacce ta mafana da horo a fannin koyon noman Zuma, ta ce, wannan shiri ta samu ilimi sosai ganin yadda Gwamnatin A A Sule ta yi tsayin daka wajen ganin ya taimaka wa matasa musamman mata domin su tsaya da kafarsu.
Sannan ta yi godiya ga Gwamnatin Shugaba Tinubu a matsayinsa na wanda ya yi tunanin yadda za a tsamo ‘yan Nijeriya daga kangin talauci.
Haka zalika Abubakar Ruth, matashiya ce da ta koyi yadda ake kera Jaka da Takalma, cewa ta yi, “A matsayinta na matashiya kuma talaka a yanzu babu abin da za ta maida hankali a kai illa ganin ya habaka wannan sana’a, inda a karshe ta yi godiya ga shugaban Kasa da kuma Gwamnan Jihar Nasarawa AA Sule bisa hangen nesansu na kokarin karfafa wa matsa musamman ma mata a wannan yanayi da ake ciki na kuncin rayuwa.”
Daga cikin wadanda suka albarkaci taron budewa da rufewa, sun hada da Babban Edita, kuma Babban Mataimaki ga Shugabar Kamfanin LEADERSHIP Mista Azubuke, da Mataimakin shugaban kamfanin Mike Okpere, sai kuma Babban Manajan Darakta Na Rukunin Kamfanin LEADERSHIP Malam Mu’azu Elazeh, da Darakta a LEADERSHIP Abraham Nda Isiah. Bayan kammala ba da wannan horo ne kamfanin LEADERSHIP na ya ba da takardar shaida ga dukkan daliban da suka samu halartar wannan horo.