Biyo bayan wa’adin da aka bai wa Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu na lalubo mafita kan yajin aikin ASSU, Kungiyar Dalibai ta Kasa (NANS), ta yi kira da a sauke ministan daga kan mukaminsa.
In ba a manta ba shugaba Muhammadu Buhari a ranar 19 ga watan Julin 2022, ya bai wa Adamu wa’adin sati biyu da ya kawo karshen yajin aikin aikin da ASUU ke yi domin daliban da ke karatu a jami’oi su koma bakin karatunsu.
- 2023: Fintiri Ya Zabi Mace A Matsayin Abokiyar Takararsa
- Kwamishinan Yobe, Goni Bukar, Ya Rasu A Hadarin Mota
Sai dai, wannan wa’adin na sati biyun ya kare ba tare da samar da wani daidaito ba, inda hakan ya janyo ASUU ta kara tsawaita yajin aikinta da sati hudu.
Da yake mayar da martani kan lamarin shugaban NANS, Kwamared Sunday Asefon, a cikin sanarwar da ya bai wa LEADERSHIP, a yau Laraba, alamu sun nuna cewa, Adamu bai da wani kwarin gwiwa wajen tafiyar da ma’aikatarsa.
Asefon, ya ci gaba da cewa, “A bisa wannan dalilin ne, muke yin tambaya kan wacce irin kwarewa ce Adamu yake da ita da har aka nada shi a mukamin Ministan Ilimi domin bai da wata tausaya wa kan abin da ya shafi matsalar daliban.
“Tun lokacin da aka nada Adamu mukamin minista, ASUU ta shiga yajin aiki na kusan watanni 18 haka fannin ilimin manyan makarantun kasar ya tabarbare.
“Ya zama wajibi mu yi kira ga shugaba Buhari da ya gaggauta sauke Adamu daga kan mukaminsa na Ministan Ilimi ya maye gurbinsa da kwararren da ya dace.”
Ya ce, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an amince da wannan bukatar tasu ta sauke Adamu daga kan mukamin nasa, inda suka a sanar da cewa, dole ne Adamu ya sauka.
A karshe dhugaban ya ce, ya zama wajbi masu kishin kasar nan su matsa wa gwamnatin tarayya lamba don a sauke Adamu daga kan mukaminsa.