Mataimakin shugaban kungiyar gaggauta cinikayya ta kasar Sin Zhang Shaogang, ya bayyana a gun taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya a yau Litinin, cewar za a kaddamar da bikin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa na Sin wato CISCE a takaice, wanda zai gudana tsakanin ranakun 26 zuwa 30 ga wata mai zuwa a nan birnin Beijing.
Bikin dake tafe, mai taken “Raya tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa, da raya makomar duniya ta bai daya cikin hadin kai”, zai mai da hankali kan kara azamar hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar wannan tsari. An yi kiyasin cewa, wakilan sassan siyasa da kasuwanci daga Sin da sauran kasashe fiye da 1000, za su halarci bikin bude baje kolin na CISCE karo na 2, wanda za a kaddamar da safiyar ranar 26 ga watan mai zuwa. Kaza lika yayin taron, za a gabatar da sanarwar ba da tabbaci ga aiwatar da tsarin a duniya. Kana za a aiwatar da ayyuka masu nasaba da shi fiye da 300.
- Xi Jinping Ya Jaddada Bukatar Gina Sin Zuwa Kasa Mai Karfin Al’adu Ya Zuwa 2035
- Kasar Sin Ta Bada Tallafin Abinci Ga Mabukata Da Na Kudin Karatu Ga Dalibai A Malawi
A karon faro na bikin, an taba gabatar da yankunan baje koli guda 5, wato na tsarin samar da makamashi masu tsafta, da tsarin samar da motoci na zamani, da na fasahohin yanar gizo, da kuma zaman rayuwa mai gina jiki, da aikin gona mai kiyaye muhalli.
Har ila yau, bikin wanda za a gudanar a wannan karo, na kunshe da wani sabon bangare bisa tushen wadannan yankuna 5 cikin hadin kai, wato yankin baje kolin tsarin samar da kayayyaki bisa kimiyya da fasaha na zamani.
Ya zuwa yanzu, kamfanonin Sin da na sauran kasashe fiye da 600, sun yi rajistar halartar bikin, adadin da ya karu da kashi 20% bisa kan na karon farko. (Amina Xu)