Gwamnatin tarayya ta jaddada ƙudirinta na aiwatar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na ₦70,000 a dukkan matakai, ba tare da nuna ɓangaranci ba.
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ne ya bayyana hakan a yau Litinin bayan wata ganawa da shugaban ƙasa Bola Tinubu, a fadarsa da ke Abuja, inda ya yabawa gwamnatocin jihohi da suka fara aiwatar da manufofin.
- Gwamnatin Borno Ta Nada Kwamitin Aiwatar Da Mafi Karancin Albashi
- Nwifuru Ya Amince Da N75000 Mafi Karancin Albashi Ga Ma’aikatan Ebonyi
Ya jaddada cewa sabon mafi ƙarancin albashin shi ne abin da gwamnatin shugaba Tinubu, ta sa gaba tare da nuna gamsuwa da matakan aiwatar da shi, inda ya nuna cewa wasu jihohi ma sun yi abun a yaba wajen wuce ma’auni na ₦70,000.
Akume ya kuma buƙaci gwamnonin da har yanzu ba su fara aiwatar da shi ba da su bayar da fifiko wajen aiwatarwa tare da fara biyan sabon mafi karancin albashin
Bugu da kari, Akume ya bayyana cewa tattaunawar da ya yi da shugaban ƙasar ta haɗa da wasu batutuwan da suka shafi gudanar da mulkin ƙasar nan.