Ƙungiyar Hezbollah ta ƙasar Lebanon, ta naɗa Naim Qassem, a matsayin sabon shugaban da zai maye gurbin, daɗaɗɗen shugabanta Hassan Nasrallah, wanda Isra’ila, ta kashe a wani harin bam a Beirut, a watan Satumba.
Sabon shugaban wanda ya riƙe muƙamin mataimakin babban sakatarenta, ya kasance ɗaya daga cikin jagororinta da suka rage a raye bayan da Isra’ila ta kashe yawancinsu a hare-hare a makonnin nan.
- Boko Haram Ta Hallaka Sojoji 40 A Chadi
- Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Gyara Wutar Lantarkin Arewa Cikin Gaggawa
Sai dai kawo yanzu babu wanda ya san inda yake zaune, duk da cewa ana raɗe-raɗin cewa yana zaune a Iran, wadda ke taimaka wa Kungiyar.
Cikin sanarwa naɗin da ƙungiyar ta fitar ta ce ta yi hakan ne bisa dogaro da Allah (SWT), tare da bin tsarin Musulunci, da ƙa’idar manufofinta, da sharuɗan zaɓe, ta na mai yi masa fatan jagoranci da alƙawarin biyayya ga Allah, da martaba babban jagoranta shahidi Sayyid Hassan Nasrallah da sauran shadidan da ta ce sun rasu.
Ƙungiyar ta Hezbollah, dai ta lashi takobin ci gaba da gwagwarmayarta na yaƙar rashin adalci da zalincin da Isra’ila ke yi har sai ta kai ga nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp