Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da Naira 71,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikatan jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Facebook a ranar Talata.
- Xi Da Shugaban Kasar Zambia Hichilema Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 60 Da Kulla Alakar Jakadanci
- Sin Za Ta Harba Kumbon “Shenzhou-19” Mai Daukar ’Yan Sama Jannati 3
Ya ce, matakin ya yi daidai da kudurin gwamnatinsa na tabbatar da adalci da inganta rayuwar ma’aikata.
“A bisa kudirinmu na tabbatar da adalci a zamantakewa da inganta rayuwar ma’aikatanmu, mun amince da Naira 71,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi a Jihar Kano.” in ji Abba
Gwamnan ya ce, sabon mafi karancin albashin zai fara aiki ne daga watan Nuwamba.