• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Minista Ya Buƙaci Masu Amfani Da Manhajojin Sada Zumunta Su Riƙa Ƙimanta Nijeriya 

by Sulaiman
12 months ago
Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga masu ƙirƙira da masu tasiri a shafukan sada zumunta da su rage munanan kalamai kan Nijeriya tare da fifita muradun ƙasar ta hanyar bin ƙa’idojin ɗa’a wajen gudanar da ayyukansu.

Idris ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin bikin Makon Ilimin Yaɗa Labarai da Bayanai na Duniya na Ƙasa na 2024 mai taken “New Digital Frontiers of Information: Media and Information Literacy for Public Interest Information” wanda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta shirya tare da haɗin gwiwar Cibiyar Ilimin Yaɗa Labarai da Bayanai ta Duniya, Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya.

  • Arewa ta fi Talakawa, Ta Cancanci Samun Karin Tallafi Mai Yawa – Minista Mai Jiran Gado
  • ‘Yan Bindiga Ba Su Karɓe Sansanin Horo Da Ke Neja Ba – Hedikwatar Tsaro

A wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, Mataimaki na Musamman ga Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai ya fitar, Idris ya jaddada muhimmancin daidaita suka da kishin ƙasa, inda ya buƙaci masu ƙirƙira a shafukan sada zumunta da su yi la’akari da muradun ƙasa yayin yaɗa bayanai.

LABARAI MASU NASABA

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Ya bayyana cewa, “Yana da muhimmanci mu riƙa suka da kuma sanya gwamnati da sauran shugabanni su yi bayani domin aikin kafafen yaɗa labarai kenan…Amma kuma yana da matuƙar muhimmanci a wajen bayar da rahoto, mu fifita muradin ƙasa.”

“Ina sake maimaitawa, ba za mu iya tsammanin girma da kuma samun mutane su zo su zuba jari a ƙasarmu ba yayin da duk abin da muke turawa waje a kowane lokaci ba shi da kyau. Akwai labarai masu kyau da yawa da ke fitowa daga Nijeriya kuma ya zama wajibi mu kasance masu kishin ƙasa yayin da muke bayar da rahoto domin Nijeriya ta kai ga inda take so ta kai na wadata da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana a kai,” inji shi.

Ministan ya yi Allah-wadai da yaɗuwar labaran ƙarya a shafukan sada zumunta, inda ya yi gargaɗin cewa, idan ba a daƙile ba, hakan na haifar da barazana ga haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Ya bayyana cewa, “Duk wanda ke da kwamfutar tafi-da-gidanka ko wayar android zai iya zama mai samar da labarai, wanda zai iya isa ga mutane masu yawa. Sai dai, wannan shimfiɗar wuri na dijital… yana haifar da matsaloli masu muni, musamman tare da yaɗuwar bayanan ƙarya.”

Idris ya yabawa UNESCO bisa ƙoƙarin da take yi na yaƙi da labaran ƙarya a Nijeriya ta hanyar kafa Cibiyar Ilimin Yaɗa Labarai da Bayanai ta Duniya.

Ya sanar da cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai tare da haɗin gwiwar Budaddiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN) na ci gaba da mayar da cibiyar ta zama Cibiyar UNESCO ta Rukuni na 2.

Wakilin UNESCO a Nijeriya, Abdourahamane Diallo, ya kuma jaddada muhimmancin shigar da Ilimin Yaɗa Labarai (MIL) cikin tsarin karatun Nijeriya.

Mataimakin Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya, Farfesa Olufemi Peters, ya gode wa Ministan bisa goyon bayan da yake bai wa jami’ar wajen ƙarfafa ayyukan Cibiyar Ilimin Yaɗa Labarai da Bayanai ta Duniya da ke cikin jami’ar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

TCN
Labarai

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

October 9, 2025
Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI
Labarai

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC
Labarai

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
Next Post
GORON JUMA’A

GORON JUMA'A

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 9, 2025
TCN

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

October 9, 2025
An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

October 9, 2025
Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.