A gobe Juma’a ne za a wallafa makalar shugaban kasar Sin Xi Jinping, don gane da bunkasa samar da isassun guraben ayyukan yi masu inganci.
Makalar ta Xi Jinping, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kwamitin soja na koli na kasar Sin, za a wallafa ta ne cikin muhimmiyar mujallar kwamitin kolin JKS mai suna Qiushi, fitowa ta 21 a shekarar bana. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp