A yau ranar 3 ga wannan wata da karfe 4 da minti 12 da yamma, kumbo dakon ‘yan sama jannati samfurin Shenzhou-18 ya rabu da turkensa na tashar binciken sararin samaniya cikin nasara.
Bisa bayanin da ofishin kula da harkokin sama jannati na kasar Sin ya yi, kafin kumbon Shenzhou-18 ya rabu da tashar, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-18 sun yi hadin gwiwa tare da ma’aikatan dake doron duniya, da kammala ayyukan daidaita tsarin tashar, da abubuwan binciken da sauransu, da mika aiki ga ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-19.
Daga bisani kumbon Shenzhou-18 zai dawo doron duniyar bayan ya samu umurni, kuma ‘yan sama jannatin kumbon wato Ye Guangfu, da Li Cong, da Li Guangsu za su dawo gida. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp