Kungiyar direbobi ta NARTO, ta nuna damuwarta a kan yadda ake ci gaba da fuskantar karancin man fetur a yankin Abuja da kewaye, ya kuma ce ya kamata al’umma su kwantar da hankalinsu don gwamnati na nan tana kokarin ganin an kawo karshen lamarin.
Shugaban kungiyar, Alhaji Yusuf Othman, ya bayar da tabbacin a tattaunawarsa da manema labarai a Legas ranar Alhamis.
- Shugaba Buhari Ya Amince Da Kara Kudin Dakon Man Fetur
- Dalilin Da Ya Sa ‘Yan Kasuwar Fetur Suka Kara Farashi Zuwa Naira 179
Ya kuma karyata maganar da wasu masu gidajen mai ke cewa wai kungiyarsu tana zagon kasa ga dakon mai da ake yi zuwa sasan Nijeriya saboda rashin kyawun hanyoyi da rashin cikkakenj jari.
“Babu gaskiya a wanna maganar, muna jin dadin aikimu kuma ana raba mai kamar yadda aka saba muna yaba wa gwamanatin tarayya a kan haka.
A kan haka ya shawarci al’umar yankin Abuja da kada su firgita saboda akwai isassan man fetur a gidajen mai kamar yadda aka saba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp