Shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai halarci taro na 31 na shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta kasashen Asiya da Pacifik wato APEC wanda za a yi Lima, tare da ziyarar aiki a kasar ta Peru, daga ranar 13 zuwa 17 ga wata, bisa gayyatar shugabar Jamhuriyar Peru, Dina Ercillia Boluarte Zegarra.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ce ta sanar da hakan a yau Juma’a. Ta kara da cewa, shugaba Xi zai kuma halarci taro na 19 na kungiyar G20 a birnin Rio de Janeiro, tare da ziyarar aiki a kasar Brazil, daga ranar 17 zuwa 21 ga wata, bisa gayyatar shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva. (Fa’iza Mustapha)
Talla