Wata tanka dauke da man fetur ta sake yin hatsari a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Nijeriya, lamarin da ya jefa al’ummar da ke kan iyaka da Jigawa da Kano cikin firgici.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba, 2024, a kusa da kauyen Gamoji, kan hanyar Kano zuwa Maiduguri. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS) a Jihar Jigawa, Aliyu M.A, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
- Babban Jami’in Sin Ya Halarci Taron Kolin Shugabannin Kasa Da Kasa Kan Daukar Matakan Daidaita Sauyin Yanayi
- Shugaba Xi Jinping Ya Tashi Daga Beijing Don Halartar Taron APEC
A cewar Aliyu, “da misalin karfe 10:43 na safe ne muka samu kiran gaggawa daga Zubairu Ahmad, Hakimin Kuho, inda ya sanar da mu wani hatsarin da wata tanka ta yi a Tsaida, Kwanar Kalle, kusa da kauyen Gamoji.
“FFS ta amsa kiran cikin hanzari, inda ta isa wurin da misalin karfe 10:50 domin kashe wutar da ta tashi.
Amsa kiran gaggawa da FFS ta yi, ya taimaka wajen dakile ƙarin asarar rayuka a irin lamarin da ya faru a baya a jihar. Har yanzu dai ba a fitar da wani rahoto a hukumance ba kan musabbabin hatsarin da kuma barnar da hatsarin ya yi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, wannan shi ne karo na biyu da fashewar tankar dakon mai a yankin ta faru cikin wata guda.
A ranar 15 ga Oktoba, 2024, makamancin haka ta faru a garin Majia da ke karamar hukumar Taura, inda wata motar dakon mai da ta taso daga jihar Kano zuwa Nguru ta jihar Yobe ta tarwatse, inda ta kashe mutane sama da 170.