Da yammacin jiya Alhamis 14 ga wannan wata agogon kasar Peru, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sauka a birnin Lima na kasar Peru, cikin jirgin sama na musamman, domin halartar kwarya kwariyar taron shugabannin kasashen mambobin kungiyar APEC karo na 31, tare kuma da gudanar da ziyarar aiki a kasar, bisa gayyatar da takwararsa ta jamhuriyar kasar Peru Dina Boluarte ta yi masa.
Jim kadan da saukarsa a filin jirgin sama, shugaba Xi ya gabatar da jawabi, inda ya isar da gaisuwa, da fatan alheri ga gwamnati da al’ummun kasar Peru. Shugaba Xi ya ce, kasashen Sin da Peru suna da dadadden zumunci, kuma Peru daya ce daga cikin kasashen Latin Amurka wadanda suka daddale huldar diplomasiyya da sabuwar kasar Sin tun kafuwarta a shekarar 1949.
- Gidauniyar Bafarawa Ta Tallafa Wa ‘Yan Zanga-zangar Tsadar Rayuwa Da Jarin Naira Miliyan 18
- Gwamnatin Nijeriya Ba Ta Runtsawa Saboda Matsalar Tsaro – Minista
Kazalika a ‘yan shekarun da suka gabata, huldar dake tsakanin kasashen biyu tana kara zurfafa sannu a hankali, kana amincin siyasarsu shi ma ya kara karfafa yadda ya kamata, yayin da ake gudanar da manyan ayyukan hadin gwiwa tsakaninsu lami lafiya. Duk wadannan suna haifar da matukar alfanu ga al’ummun kasashen biyu.
Shugaba Xi ya kara da cewa, yanzu haka ana cike da imanin cewa, a karkashin kokarin da sassan biyu suke yi, ziyararsa za ta daga huldarsu zuwa wani sabon matsayi. A sa’i daya kuma, Sin za ta ingiza ci gaban hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban. Ya ce “Ina son yin kokari tare da bangarorin da abin ya shafa, domin ba da sabuwar gudummowa ga raya tattalin arziki mai bude kofa na yankin Asiya da tekun Pasifik, da ingiza karuwar tattalin arzikin duniya, da kuma gina kyakkyawar makomar bai daya ta kasashen yankin.” (Mai fassara: Jamila)