A lokacin da Kwamared Dr. Nasir Idris ya dare kujerar gwamnan Jihar Kebbi a matsayin gwamna na 9 a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ya zo da niyyar sake fasali a fannin ilimi. Gwamna Idris wanda aka fi sani da Kauran Gwandu, ya fito a matsayinsa na tsohon malami kuma dan kungiyar kwadago domin magance wasu matsalolin da suka addabi jihar. A karkashin jagorancinsa, Kebbi na ci gaba da bunkasa ta fannin ilimi da nufin yakar jahilci, inganci, gwarin gwia da kuma kafa jihar a matsayin cibiyar koyar da ilimi. Yunkurin nasa bai tsaya ga dalibai da malamai kadai ba, har ma da sake farfado da cibiyoyi na kashin kansu wanda hakan ke nuna jajircewarsa ta ganin an samar wa Kebbi kyakkyawar makoma.
Muhimmantar Da Jin Dadin Malamai
Gwamna Idris ya fahimci mahimmancin malamai wajen samar da ingantaccen ilimi, kuma ya aiwatar da gyare-gyare da yawa don karfafa musu. A wani mataki da malamai suka yi maraba da gwamnan, gwamnan ya kara shekarun ritayar malamai daga shekara 60 zuwa 65 sannan ya kara wa’adin aiki daga 35 zuwa 40. Wannan manufa tana ba wa kwararrun malamai damar ci gaba da aiki na tsawon lokaci, tare da samun kwanciyar hankali a cikin aji. Bugu da kari, domin magance matsalar karancin malamai, gwamnati ta amince da daukar sabbin malamai 2,000 a fadin jihar. Wadannan yunkurin ‘yar mununiya ce kan yadda Idris ya mayar da hankali wajen gina kwararrun ma’aikata masu koyarwa don tallafa wa ingantaccen ilimi ga matasan Kebbi. Domin kara kwadaitar da malamai, gwamnatin Idris ta kara albashin malamai, tare da amincewa da bukatar su domin karfafa musu. Wadannan tsare-tsare na nuni da gagarumin sauyi na fahimtar kokarin malamai a matsayin masu kawo ci gaban al’umma.
Samar Da Kayan Aiki Da Karin Manyan Makarantu
Daya daga cikin manyan tsare-tsaren ilimi da gwamnan ya yi sun hada jajircewarsa kan sake fasalin makarantun. A baya bangarorin ilimi na Jihar Kebbi ya tabarbare ta hanyan lalacewar ajujuwa da yawa, amma a karkashin jagorancin Idris, ana magance wadannan matsaloli cikin tsari. Jim kadan bayan hawansa kujerar mulki, ya kaddamar da manyan gyare-gyare a makarantun firamare, sakandare, da makarantun gaba da sakandire, inda ya kashe Naira biliyan 8.9 wajen ginawa da inganta makarantun sakandire 120. Bugu da kari, an bayar da kwangilar gina manyan makarantu guda hudu, daya a kowace majalisar masarautu hudu na jihar, wadanda za su zama cibiyoyi masu inganci da aka tsara don yin koyi da kyawawan halaye a wuraren koyo. Wadannan abubuwa na habaka kayan aikin ba an yi su ne domin kwalliya ba, a’a an sanya su ne domin samar da kyakkyawan yanayi don inganta koyo, tare da sabbin ajujuwa, sabbin kayan aiki na zamani, dalibai da malamai suna amfana daga wannan tsari na samar da ingantaccen ilimi.
Fadada Hanyoyin Samun ilimi Musamman Ga ‘Yan Mata
Babban abin da gwamnatin Gwamna Idris ta mayar da hankali a kai shi ne, kara samun damar ba da ilimi, musamman ga yara mata. A jihar da a wasu lokuta al’adun gargajiya na iya hana ‘ya’ya mata damar samun ilimi, gwamnan ya ba da gudummawa sosai a shirye-shiryen da ke inganta hada jinsi. Tallafin da gwamnatinsa ke bayarwa ya janyo karuwar shigar mata makarantu, tare da kawar da abin da ya yana kare su ga barin samun ilim da kuma samar da damammaki na ilimi. Domin nuna jajircewarsa, Gwamna Idris ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 50 ga Makarantar Sakandaren Kimiyyar ‘yammata ta Command, Goru, al’amarin da ke nuna himmar gwamnatinsa wajen ciyar da ilimin yara mata gaba. Wannan jarin yana nufin magance bukatu na gaggawa tare da tallafawa inganta abubuwan more rayuwa wadanda za su amfani tsirarrun dalibai mata masu zuwa. Bugu da kari, domin rage wa iyalai matsalolin kudi, gwamnatin jihar ta biya kudaden jarrabawar NECO da WAEC, wanda hakan ke kara habaka dalibai a wadannan muhimman abubuwan tantancewa.
Samar Da Tallafin Ilimi Ga Daliban Manyan Makarantu
Ajandar sake fasalin ilimi na Gwamna Idris ya wuce karatun firamare da sakandare, domin gwamnatinsa ta yi alkawarin fitar da kudi masu yawa don tallafa wa dalibai a manyan makarantu, wanda ya shafi rajista da kuma kudin makaranta. A wani muhimmin mataki da gwamnatin ta dauka ta biya Naira biliyan biyu ga daliban da suka yi rajista a jami’o’in Nijeriya, sannan ta ware Naira miliyan 723 ga daliban Jihar Kebbi da ke karatu a kasashen waje, a kasashe irin su Indiya, Masar da Cyprus. Ta hanyar tabbatar da tallafin kudi ga manyan makarantu kuwa, Gwamna Idris yana taimakawa wajen gina hazikan mutane masu ilimi, kwararrun wadanda suke a shirye don bayar da gudummawar ci gaban jihar.
Daukaka Darajar Manyan Makarantun Jihar
Wani babban abin farin ciki da aka samu a zamanin mulkin Idris shi ne, ci gaban da aka samu a fannin ilimin manyan makarantun Kebbi.
Gwamnan ba wai kawai ya inganta fannin kudade bane, har ma ya cike gibin hukumomin da suka dade suna hana ci gaba. A farkon tarihi, gwamnatin Idris ta kafa hukumomin gudanarwa ga dukkan manyan makarantun jihar, ciki har da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi, Aliero (KSUSTA), da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar, Dakingari. Wannan ya nuna mafarin tsarin tafiyar da mulki wanda zai kawo karshen rikon sakainar kashi da tabbatar da alkibla ga wadannan cibiyoyi. Haka kuma, a karon farko tun bayan kafuwarta sama da shekaru 30 da suka gabata, KSUSTA ta gudanar da taro wanda gwamnatin jihar ta dauki nauyin gudanar da ayyukanta.
Wannan ci gaba yana wakiltar sabuwar fahimtar mahimmancin bikin nasarar ilimi da karfafa cibiyoyin al’adu. Har ila yau, gwamnatin Idris ta daukaka darajar Makarantar Fasahar Lafiya ta Jega zuwa Kwalejin, tare da bayar da kudade don amincewa da kwasa-kwasanta daga kwararrun mata wadanda aka fitar da su don tabbatar da kwasa-kwasan karatunta, wanda hakan ya kara daukaka martabar makarantar da kuma kyawunta ga dalibai masu zuwa.
Bunkasa Makarantun Tsangaya Da Rage Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta
Yunkurin da gwamnan ya yi na kawar da jahilci ya hada da tallafa wa makarantun Tsangaya (Alkur’ani) inda a baya yara da dama ke shafe kwanakinsu ba tare da samun damar zuwa makaranta ba.
Ta hanyar samar da kudade da kokari na zamani, wadannan makarantu yanzu suna canzawa don ba da daidaitaccen tsarin karatu wanda ya hada da kwarewar karatu da kididdigewa.
Sakamakon shi ne tsarin ci gaba wanda ke mutunta al’adun gargajiya tare da ba wa yara dabarun tushen da suke bukata don bunkasa a cikin zamantakewar zamani. Wannan garambawul ya kuma rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Kebbi, tare da magance matsalar da ta dade tana addabar jihar.
Samar Da Tsarin Sanya Ido A Kan Yadda Ake Tafiyar Harkar Ilimi A Jihar
Sanin cewa gyare-gyaren ilimi mai dorewa na bukatar sa ido, Gwamna Idris ya sake farfado da bangaren bincike da sanya ido da ke cikin ma’aikatar ilimi. Wannan yunkuri na da nufin tabbatar da daidaito da kula da inganci a duk makarantun da ke Kebbi, tare da aiwatar da ka’idodin da suka dace da hangen nesa na gwamna na inganta fannin ilimi.
Tare da sabunta mayar da hankali kan lissafi da ci gaba da ingantawa, sashen ilimi na Kebbi yana da kyakkyawan matsayi wajen samar da sakamako mai kyau.
Tsayayyen Kuduri A Kan Bunkasa Ilimi
Cikin kasa da shekaru biyu Gwamna Idris ya dauki wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba wajen tunkarar kalubalen da ake fuskanta a bangaren ilimi na Kebbi. Tare da zuba jarin sama da Naira biliyan 10 a fannin ilimi, gwamnatinsa ta bar tarihi a fannin ilimi, jin dadin malamai, da tsarin tallafawa dalibai.
Ta hanyar kawar da matsalolin kudi, fadada hanyoyin samun dama da zamanantar da ababen more rayuwa, Idris ya samar da yanayin da dalibai daga bangarori daban-daban za su iya samun ingantaccen ilimi.
A karkashin Gwamna Nasir Idris, Jihar Kebbi ba ta gamsu da matsayin da ta samu a baya ba idan aka kwatanta da ma’aunin ci gaban bil’adama; tana ci gaba da tafiya sannu a hankali domin zama ingantacciyar cibiyar ilimi a Nijeriya. Gyaransa na sake fasalin abin da zai yiwu ga makomar Kebbi, yana ba wa matasa kayan aikin da suke bukata don bunkasa da kuma ba da gudummawa ga al’umma. Nasarorin da gwamnan ya samu sun nuna tsantsar kudurinsa na son ci gaba, ta yadda Jihar Kebbi ta zama jihar da kowane yaro ke da damar koyo, girma, da samun nasara.