Gwamnatin tarayya ta dage takunkumin da ta kakaba wa masu yi wa kasa hidima (NYSC) zuwa masana’antu masu zaman kansu, wanda hakan zai bai wa masu hidimar damar yin aiki a masana’antu kamar su banki da masana’antun mai da iskar gas.
Wannan sabon sauyin, wanda Ministan Ci gaban Matasa, Ayodele Olawande ya sanar, zai fara aiki ne akan masu hidima na 2024 Batch ‘C’.
- Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Babban Limamin Masallacin Minna
- Bangaren Sin Ya Yi Kiran Tsagaita Bude Wuta A Sudan Cikin Hanzari
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai kwanan wata 18 ga Nuwamba, 2024.
Wannan sabon tsarin, ya soke wani tsari ne da ya takure masu hidima ga kasa a bangaren fannin ilimi, noma, lafiya, da ababen more rayuwa kawai.
Wannan tsarin, wanda aka bullo da shi a lokacin tsohon Ministan Matasa, Bolaji Abdullahi, ya yi kokarin kiyaye darajar masu yi wa hidima kasa domin hana kamfanonin masu zaman kansu wulakanta su.
Sai dai, wannan sabon tsarin zai fara aiki ne a Legas da Abuja, inda za a tura masu yi wa kasa hidima zuwa masana’antu masu zaman kansu da suka hada da zababbun bankuna da kamfanonin mai da iskar gas.