Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce batun da ya shafi yankin Taiwan, batu ne mai muhimmanci cikin muradun kasar Sin, kuma manufar kasar Sin daya tak, matsaya ce da dukkan kasashen duniya suka amince da ita.
Lin jian ya bayyana haka ne yau Laraba yayin taron manema labarai da aka saba yi kullum, lokacin da yake tsokaci game da tafiyar da babban jami’in sashen kula da harkokin wajen Taiwan ya yi zuwa nahiyar Turai, inda ya ce amincewa da manufar Sin daya tak, ita ce tubalin dangantakar Sin da Turai. Yana mai cewa, Sin na adawa da duk wani nau’i na musaya tsakanin kasashen dake da huldar diflomasiyya da ita, da kuma yankin Taiwan.
Baya ga haka, da ya tabo tsokacin da wasu kasashe suka yi game da batun Jimmy Lai, kakakin ya ce Hong Kong wuri ne dake tafiyar da harkokinsa bisa tsarin doka, kuma ka’idar ita ce dole a tabbatar da doka kuma a gurfanar da mai laifi. Ya ce babu wanda zai aikata laifi bisa fakewa da neman ’yanci sannan kuma ya nemi tserewa fushin doka. Kakakin ya kara da cewa, Jimmy Lai shi ne babban mashiryin hargitsin adawa da Sin a Hong Kong kuma ya shiga an dama da shi, kana kuma, dan aiken masu adawa da kasar Sin. Har ila yau, Lin jian ya ce gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, na goyon bayan yankin musammam na Hong Kong wajen kare tsaronsa da kuma hukunta duk wani laifi dake barazana ga tsaro bisa doron doka. (Fa’iza Mustapha)